Sallar gawa a musulunci | |
---|---|
prayer (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | Sallah |
Bangare na | funeral (en) |
Sunan asali | صَلَاةُ الْجَنَازَةِ |
Vocalized name (en) | صَلَاةُ الْجَنَازَةِ |
Addini | Musulunci |
Muhimmin darasi | Islamic view of death (en) |
Mabiyi | Islamic funeral (en) , Absolution of the dead (en) da shroud (en) |
Ta biyo baya | funeral procession (en) da burial (en) |
Salatal Janazah ita ce sallar jana'izar Musulunci; wani bangare na ibadar jana'izar Musulunci. Ana yin sallar ne a cikin jam’i domin neman afuwar mamaci da dukkan musulmin[1] da suka rasu. Sallar Janazah farilla ce gama-gari a kan musulmi (farḍ al-kifaya) wato idan wasu musulmi suka dauki nauyin yin ta, wajibi ne ya cika, amma idan babu wanda ya cika, to dukkan musulmi za su yi hisabi.[2]
Yin Sallar Jana'iza a lokacin da gawa ba ya nan gaba daya bai halatta a mazhabar Hanafiyya da Malikiyya ba, an halalta a mazhabar Hanbaliyya, kuma ana so a cikin mazhabar Shafi'iyya.[3]